Bayan kama jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood Sadiya Haruna da Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi, tare da gurfanar da ita a gaban Kotu, da zartar mata da hukuncin koma wa makarantar Islamiyya, don ta kara samun ilimin addinin Muslunci.
Kawo wa yanzu dai, jarumar ta fito ta bayyana hukuncin da aka zartar a kanta da cewar shi ne mafi alheri a rayuwar ta. Jarumar ta bayyana hakan ne a harabar Ofishin Hukumar Hisbah a lokacin da take tattauna wa da yan jarida cikin su har da wakilin Jaridar Dimukaradiyya.
Sadiya Haruna ta ce, komawar ta Islamiyya da kuma wa’azin da aka yi mata ya sa ta yi tuban da ya kai ta ga yin nadama a kan abin da ta aikata a baya.
in da take cewa “Abubuwan da na rinka fada da kalmomi a yanzu na gano ya saba wa koyarwar addinin Muslunci, kuma hukuncin da aka zartar mun, na gamsu da shi, kuma ina godiya a gare su Ubangiji Allah ya saka musu da alheri, Allah ya kara musu nisan kwana.” Inji ta.
A nashi bangaren Kwamandan Hukumar Hisbah Sheikh Sani Ibn Sina a kan maganar cewa ya yi “Mu duk wanda ya bayyana tuban sa to in Allah ya yarda za mu karba, kuma za mu yi masa afuwa, muna fatan Allah ya sa ta shiryu kuma ta gane, tun da har ta fito ta iya cewa hakan da aka yi mata an yi don gyaran tarbiyyar ta ne to Allah ya sa. Amma hakan ba zai sa mu yi kasa a Gwuiwa ba, muna ci gaba da bibiya, kuma ba ita kadai ba da makamantan masu aiki irin nata. “a cewar shi.
Sai dai kuma a ta bangaren Hukumar gidan yari, ta bayyana cewar, akwai bukatar a Kara yin nazari dangane da makarantar da Sadiya Haruna take zuwa, domin ba kullum makarantar ta ke zama ba, domin kotun ta yanke hukuncin za ta rinka zuwa makaranta kullum tare da samun rakiyar Gandiroba, wanda zai rinka yi mata rakiya.
Kazalika hukumar ta ce, amma an gano makarantar ba kullum take zama ba.
A nashi jawabi Jami’in hulda da jama’a na hukumar gidan yarin, Misbahu Lawan Kofar Nassarawa ya ce, “Yanzu Jami’an mu za su kalli cewar, an koya mata addini, don haka za mu saka ido mu ga yadda za a koya mata addini kamar yadda Kotu ta yi umarni. Wannan shi ne halin da a ke ciki a yanzu, don haka za mu ci gaba da saka ido, don ganin an bi umarnin da Kotu ta bayar. ” a cewar shi