Kano: Hisbah Ta Haramta Amfani Da Kalmar “Black Friday”

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta haramta amfani da kalmar Black Friday ga Kafafen ya?a labarai da sauran da sauran jama’a baki daya, inda ta bukaci wata tashar radiyo da ta janye amfani da Kalmar ‘Black Friday’ wato “Ba?ar Juma’a a jihar.

Black Friday kan kasance a ranar Juma’a ta hudu a watan Nuwamba inda ‘yan kasuwa ke zabtare farashin kayayyaki ga abokan cinikinsu gabannin bikin Kirsimeti.

A wata wasika mai kwanan wata 26 ga watan Nuwamba da Hisba ta rubuta zuwa ga manajan tashar Cool FM a Kano, Abubakar Ali, wani jami’in Hisbah a madadin kwamanda Janar, ya ce mafi al’ummar jihar Kano Musulmai ne wadanda ke kallon ranar a matsayin rana mai tsarki, ya fada ma manajan cewa a kan haka, tashar radiyon ta daina amfani da Kalmar “Black Friday” ba tare da bata lokaci ba.

Takardar ta kuma nuna cewa Black Friday barazana ce ga tsaro da zaman lafiyar jihar Kano. Hukumar a cikin wasikar ta ce: “Muna bayyana damuwa kan ayyana Juma’a a matsayin Black Friday, kuma ya kamata a fahimci al’ummar Kano Musulmi ne da suka ?auki Juma’a babbar rana.”

“Don haka Hisbah na son a daina kiran Juma’a Black Friday cikin gaggawa, kuma a kula cewa jami’an hukumar za su kasance a girke domin kula da lamura domin gudun afkuwar kowane irin abu na rashin da’a da kuma wanzar da zaman lafiya da aminci a jihar.

Related posts

Leave a Comment