Zancen kama wani jam’in hisba a Hotel da matar aure a wannan mako ya tayar da kura, zancen ya yi ta yaduwa kamar wutar daji a lokacin hunturu, da yawan masu tsokaci game da batun, da sun san hakikaninsa da ba su kasance suna fadin abin da suke fada ba.
Jami’in da ake zargi ba boyayye ba ne, a baya shi ne jagoran bangaren jami’an da suke operation din hana karuwanci da mayar da karuwai wajen iyayensu, wanda hakan ya sa jami’in ya yi bakin jini matuka a wurin masu gidajen da ake iskanci da sauran wuraren da ake sheke aya.
Ita yarinyar da ake magana tabbas matar aure ce, ko wata biyu ba ta yi a gidan mijinta ba. Kuma fitinanniyar yarinya ce. Babanta aminin jami’in ne matuka domin jami’in ne ma ya daura mata aure. A kankanin lokacin da ta yi a gidan mijinta sun sami sabani fiye da lissafi, daga karshe ma sai ta fice daga gidan mijin nata ta tafi sabon gari, daga baya kuma sai ta koma hotel, sai labari ya zo wa wannan jami’in cewa wance ta bar gidan mijinta an gan ta hotel kuma ta na daki mai lamba kaza, wanda hakan ya saka jami’in zuwa hotel don ya yi magana da yarinyar ya dawo da ita wajen iyayenta a matsayinsa na waliyinta, sanda ya je ashe wasu bata gari da suke jin haushin sa sun hada baki da jami’an ‘yan sanda. Shigarsa hotel din ke da wuya sai jami’an suka kama shi, su kuma ‘yan jarida ba tare da bincike ba suka hau yada labarin cewa an kama shi da matar aure a hotel wanda har wasu gidajen jaridu a Kudu suke yin batanci ga addinin musulunci, ba su kadai ba, har da matsiyatan cikinmu ‘yan dadi arna wadanda ke bakin ciki da aikin hukumar hisba na yaki da mummuna suma na yada cewa an kama jami’in hisba yana aikata iskanci.
A shari’ar musulunci babban laifi ne kawai don ka ga namiji ya shiga dakin macen da ba muharramarsa ba ka yada cewa sun yi zina, shari’a cewa ta yi a yi wa wanda ya aikata hakan bulalar kazafi, domin bai gan su turmi da tabarya suna aikata abin da yake yadawa ba. Kamar haka yake a wannan lamari jami’an tsaron da suka kama shi ba su bayar da bayanin cewa sun kama shi yana aikata wani abun Allah wadai ba kamar yadda jama’a ke yadawa.
Kafin na saki wannan rubutu sai da na yi zuzzurfan bincike game da wannan lamari, wanda na sha alwashin bayyanawa jama’a gaskiya ko da gaskiyar ba za ta yi wa hukumar ta hisba dadi ba.
Masu yi wa musulunci da shari’a isgili su fahimci cewa don jami’in hisba ya aikata ba daidai ba, hakan ba ya nufin dukkan ‘yan hisba suna aikata haka, kamar yadda ba ya nufin duk wani mai yaki da barna da umarni da kyakkyawa da aikata hakan.
Domin tabbatar da gaskiya babban Kwamandan rundunar hisban na jihar Kano Haruna Muhammad Ibn Sina ya kafa kwamitin da zai yi bincike a kan wannan batu, kuma hukumar a shirye take ta zartar da hukunci daidai da abin da binciken kwamitin ya bayar.
Allah ya bayyana gaskiya
Daga Indabawa Aliyu Imam