Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umarnin gafara ga dukkan daliban da suka shiga zanga-zangar da aka yi a kwalejin kimiyya na Dawakin Tofa da ke jihar Kano.
A wata takardar da Lauratu Ado Diso, babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta sa hannu a ranar Alhamis, ta ce Gwamnan ya bai wa ma’aikatar ilimi ta jihar umarnin.
Ya ce a dawo da daliban aji shida na makarantar domin su rubuta jarabawar kammala sakandire, jaridar Sun ta ruwaito.
Wannan takardar ta fita ne dauke da kwanan wata 12 ga watan Augustan 2020, bayan an mika takardar ga kwamishinan ilimi na jihar, Muhammadu Sanusi S. Kiru, kafin a fara taron majalisar zartarwa ta jihar.
A takardar, gwamnan ya kara da jan kunnen daliban da su kasance masu bin doka don tabbatar da cewa irin wannan lamarin bai sake faruwa ba a makarantar duk rintsi.