Kano: Ganduje Ya Rantsar Da Sabbin Alƙalai

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya rantsar da sabbin alkalai shida a babban kotun jihar Kano domin rage jinkirin da ake samu wurin yanke shari’a.

Kwamishinan Shari’a na jihar Muhammad Lawal, ne ya bawa sabbin alkalan rantsuwar kama aiki a ranar Juma’a a birnin Kano.

Sabbin alkalan da aka rantsar sune:

Abubakar Maiwada

Maryam Sabo

Zuwaira Yusuf

Jamilu Sulaiman

Sunusi Ma’aji

Hafsat Yayha Sani.‎

Ganduje ya ce an rantsar da sabbin alkalan ne saboda kwazonsu da jajircewa bayan sun yi nasarar cin gwajin da aka musu kuma kwamitin koli na alkalai na kasa, NJC, ta amince a nada su.

Gwamnan ya ce nadin da aka yi musu zai kara adadin alkalai a jihar kuma hakan zai rage tsawon lokacin da ake dauka kafin yin sharia tare da bawa alkalan daman samun natsuwa suyi adalci.

Ganduje ya bukaci sabbin alkalan su kasance masu riko da gaskiya da amana su kuma kare mutunci da kimar aikin alkalanci.

Gwamna Ganduje ya kuma rantsar da Alhaji Aminu Bahaushe a matsayin sakataren dindindin aka kuma tura shi zuwa ma’aikatar gidaje da sufuri kamar yadda kamfanin dillancin labaran NAN.

Labarai Makamanta

Leave a Reply