Bayan kimanin watanni shida da sauke tsohon kwamishanan ayyukan jihar Kano, Muazu Magaji, kan murnar mutuwar marigayi Abba Kyari da yayi, an dawo da shi cikin gwamnati dumu-dumu.
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya sake nadashi shugaban kwamitin ayyukan bututun mai da masana’antu.
Hakan na kunshe cikin jawabin da Uba Abdullahi, mai magana da yawun Sakataren gwamnatin jihar, ya wallafa.
Idan jama’a basu manta ba Ganduje ya sallami Muazu Magaji bayan ya yi jawabin da aka fassara a matsayin murnar mutuwan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari. Abba Kyari ya rasu a watan Afrilu bayan kamuwa da cutar Coronavirus.
Daga baya shima Allah ya jarabceshi da kamuwa da cutar amma ya samu saukin bayan jinya a cibiyar killace masu cutar.
Tuni ya bada hakuri bisa furucin da yayi a lokacin kuma ya yi nadamar hakan.
Mayar da Muazu Magaji ya biyo bayan mayar da Salihu Tanko Yakassai, wanda aka fi sani da Dawisu, bakin aikinsa na babban hadiminsa na kafafen yada labarai.