Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta amince da a bude makarantu a jahar Kano inda za a buɗe su daga 11 ga watan Oktoba.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Sunusi Muhammad Kiru ne ya sanar da hakan a yau.
Ya bayyana cewa ‘yan aji shida da biyar na firamare za su koma makaranata a ranar 11 ga watan Oktoban 2020.
‘Yan aji ɗaya da biyu kuma za su rinƙa zuwa makaranta a ranakun Litinin da Talata kawai, inda za su fara daga 12 ga watan Oktoba.
Sai kuma ‘yan aji uku da huɗu da biyar na makarantun firamare su ma za su rinƙa zuwa Laraba da Alhamis da Juma’a inda za su koma 12 ga watan Oktoba