Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Kano: Ganduje Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori Huɗu

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da nadin manyan sakatarori hudu a ma’aikatun gwamnatin jihar. Ganduje ya yi kira ga manyan jami’an gwamnatin da aka nada da su zamo masu ‘kwazo da jajircewa wajen sauke hakkokin da ya rataya a wuyansu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na gwamnatin jihar, Abba Anwar, ya fitar a ranar Alhamis, 24 ga watan Satumba.

Jawabin ya yi kira a gare su da su inganta ayyukansu, inda ya jaddada cewa, “dole ne ku bi ka’idoji masu nagarta irin na manyan kasashen duniya a matsayinku na manyan jami’an gwamnati a jihar”.

Sakatarorin da aka nada sune; Fatima Fulani Sarki Sumaila, Umar Liman Albasu, Kabiru Sa’idu Magami da kuma Abba Mustapha Dambatta.

Sanarwar ta ce gwamnan na umartar sabbin manyan sakatarorin da su kara himma da kiyaye mutuncin aikinsu. Har ila yau ya kuma horesu da su kasance abin koyi ga sauran kananan ma’aikatan gwamnatin masu tasowa.

Exit mobile version