Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sanya hannu akan fitar da naira miliyan 257 wajen biyan kudin makaranta dana abinci ga dalibai 43 na jihar da za su tafi karatu kasar Misra.
Sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis a Kano.
Anwar ya ce gwamnatin jihar Kano ce ta dauki nauyin daliban domin su yi karatu a fanni daban-daban a jami’ar Al-Mansoura da jami’ar October 6 duk dake kasar ta Misra.
“Haka kuma gwamnan ya sanya hannu akan biya naira miliyan 48 ga daliban da za suyi karatu a jami’ar October 6 dake kasar ta Misra,” Anwar ya bayyana cewa gwamnan ya yafewa daliban duk da shiga harkar siyasa da suka yi.
“37 daga cikin daliban da za suyi karatu a Al Mansoura, sun rubuto takarda ga gwamna akan ya yafe musu, kan cewa suna dana sanin yadda aka yaudare su a harkar siyasa.” A cewar shi, gwamnan ya kuma dauki wasu aiki, inda za su dinga bin diddigin yadda ake biyan alawus-alawus na daliban cikin gida, domin magance wahalar da suke fuskanta kan cutar COVID-19.
Anwar ya kara da cewa an umarci hukumar kula da karatun daliban ta jiha da ta fara yiwa daliban rijista, inda ake sa ran za a biya musu kudin makaranta kafin a bude makarantu.