Kano: Da Tsohon Saurayina Na Fara Yin Garkuwa – Mai Garkuwa

Rundunar yan sandan Jihar Kano a ranar Laraba ta cafke wasu masu garkuwa da mutane su hudu cikin su har da mace yar shekara 23, Maryam Mohammed, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ta shaida cewa aikin ta na farko a matsayin mai garkuwa da mutane ya fara ta kan tsohon saurayin ta wanda yaki auren ta bayan shafe shekaru suna soyayya.

Maryam Mohammed, wanda aka fi sani da Hajiya, an kama ta a ranar Talatar da ta gabata tare da wasu mutane uku yan tawagar ta a unguwar Jaba, karamar hukumar Ungogo da ke Jihar Kano, lokacin da suke tattaunawa da iyalan daya daga cikin wanda suka sace akan kudin fansa.

Ta ce kawun ta ne ya fara jefa ta a harkar, wani Hamza Dogo na kauyen Butsa, karamar hukumar Gusau a Jihar Zamfara, bayan sun rabu da tsohon saurayin ta.

Labarai Makamanta