Hukumar Jin dadin Alhazai ta kasa ta bayyana Hukumar Jihar Kano a matsayin hukumar dake kan gaba bisa sauran jihohin kasar, sannan ta kara da cewa hukumar na kula da kuma tabbatar da hanya mafi sauki ga Alhazan jihar.
Wannan na kunshe ne cikin jawabin da Babban shuguban Hukumar jin dadin Alhzan ta Kasa Mallam Zikurullah kunle Hassan, bayan ziyar da ya kaiwa mai girma Gwamnan Kano Dr. Abdullahi umar Ganduje a masaukin sa bayan kammala taron Koli a fadar Mulki ta Aso a ranar Litinin din nan.
Shugaban Hukumar ya bayyana yadda suke hada kafa da kafada wajen tabbatar da kyakkawar alaka a tsakanin Hukumar ta kasa daka jihohi dan jin dadin Alhazai. Ya kara da cewa “kano wata kusa ce idan aka zo zancen gudanar da Jigilar alhazai a kasa”
A na sa Martanin Gwamna Ganduje yace Hukumar Kula da Aikin hajjin ta kasa kano gida ce a gareta, sabida ko a tarihi ma Kano wata Cibiyar Aikin hajji ce ta kasa.
A wata takarda da mai Kula da watsa Labaran Gwamnan Ya rabawa manema labarai “gwamnan Ya bayyana yadda Mutane suke zuwa hajjin a Dokuna da Jakkai. Gwamnan ya kara da cewa zasu yi aiki kafada da kafada da hukumar ta kasa koda yaushe.
Dukka da dai wacar shekarar data shude babu jigilar alhazan sakamakon Annobar Korana, duk wanda suke bukatar kudaden hajjinsu an mayar misuda shi, wanda kuma zasuyi ajiya a ringa anyi misu tanadi inji Gwamnan.