Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani Aminu Musa Abdullahi, ɗan wa ga tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
An tattaro cewa an sace Abdullahi, wanda aka fi sani da Yaya Baba yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kano kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a makon da ya gabata.
Kodayake babu wani tabbaci daga rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano amma wata majiya mai tushe ta ce iyan uwan sa basu so maganar ta fita, majiyar Hausa Daily Times ta jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Majiyar, wacce ke da kusanci da tsohon sarkin, ta ce masu garkuwar sun tuntubi iyalinsa don neman kudin fansa. Amma, ba a bayyana adadin ba.
A halin yanzu an bayyana cewa ƴan uwan sun tara kuɗin fansa amma sun daina samu masu garkuwan a waya.
Direbobin da ke bin babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna suna cikin fargaba bisa sake dawowar masu satar mutane a hanyar.
Sun bayyana cewa masu garkuwan na fara aiki galibi tsakanin 5 na safe zuwa 7 na safe da 7 na yamma da 9 na yamma.
-Majiya Hausa Daily Times