Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Rundunar tsaro ta hadin gwiwa da ta hada da sojoji, ƴansanda, SSS da NSCDC, sun kama shugabannin kananan hukumomin Ungogo da Rimingado na jihar Kano, Abdullahi Ramat da Munir Dahiru da bindigu.
Wata majiyar sirri ta jami’an tsaro ta shaidawa DAILY NIGERIAN cewa an kama mutanen biyu ne a lokacin da su ke jagorantar ƴan daba domin su kai farmaki kan ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, a hanyar Zariya, Kano.
“Rundunar tsaron ta hadin guiwa
na tsaka da sintiri na tauna tsakuwa a lokacin da su ka ci karo da shugabannin da ke jagorantar ‘yan daba. Nan take jami’an tsaro su ka karɓe bindigogin daga hannun ciyamomin tare da cafke ‘yan baranda sama da 100 da suka yi wa dan takarar jam’iyyar NNPP kwanton bauna.
Majiyar ta kara da cewa, “A halin yanzu ana tsare da su a sashin binciken manyan laifuka, kuma jami’an tsaro na hadin gwiwa na ci gaba da sintiri a cikin birnin domin gurfanar da wadanda suka aikata laifin.”