Majalisar zartarwa ta Jihar Kano ta amince da kashe naira biliyan kusan tara (N8, 980, 303, 460.63) domin gina gada mai suna Muhammadu Buhari a kan Titin Maiduguri da ke ?waryar birnin na Kano.
Majalisar ta amince da kashe ku?in ne jim ka?an bayan kammala zamanta na mako-mako a ?akin taro na Africa House da ke fadar gwamnatin jihar.
Kwamishinan Ya?a Labarai Muhammad Garba ya ce wannan yun?uri na cikin burin gwamnatin Abdullahi Ganduje na gina tituna da hanyoyi domin mayar da Kano “hamsha?in birni” da kuma ha?aka harkokin kasuwanci.
A cewarsa: “Kasancewarsa birni mai tasowa kuma cibiyar kasuwanci a Najeriya, Kano na samun ?aruwar ‘yan kasuwa da ke shigowa, abin da ya sa ake bu?atar sake tsarawa da ha?aka tituna don ya iya ?aukar masu zirga-zirga a cikinsa.”
A makon da ya gabata ne tsohon gwamna kuma jagoran adawa a jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki aikin gadar, yana mai cewa “mutanen Kano sun fi bu?atar ilimi” ba gada ba.
Kazalika, kwamishinan ya ce majalisar ta amince da kashe naira miliyan 44,300,000 domin yi wa Kwalejin Harkokin Noma ta Audu Bako da ke ?aramar Hukumar Dambatta kwaskwarima.