Kano: An Soke Dukkanin Bukukuwan Sallar Layya

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da dakatar da duk wasu bukukuwan da za’a yi a yayin bukukuwan babbar sallah mai zuwa a kokarin hana yaduwar COVID-19 a cikin jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai na hadin gwiwa a jihar.

A cewarsa, za a gudanar da sallar tare da yin biyayya ga ka’idojin da aka gindaya na masana lafiya.

Muhammad Garba yaci gaba da cewa dukkan masarautun jihar Kano guda hudu da suka hada ds na Gaya, Karaye, Bichi da Rano za su gudanar da salloli a masarautunsu. Amma babu bukukuwan hawan sallah na al’ada da aka saba gudanarwa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply