Kano: An Shiga Makoki Na Rasuwar Mahaifiyar Sarkin Kano

Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar an shiga juyayi da makoki biyo bayan rasuwar Hajiya Maryam Ado Bayero matar tsohon sarkin Kano marigayi Ado Bayero, kuma mahaifiya ga Sarkin Kano na yanzu Aminu Ado Bayero.

Hajiya Maryam Bayero wadda ake wa la?abi da sunan Mai Babban Daki mahaifiya ce ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Majiyoyi daga masarautar ta Kano sun tabbatar da labarin rasuwarta, sun ce ta rasu ne a ranar Asabar a wani asibitin kwararru dake birnin Alkahira na ?asar Masar.

Majiyoyin sun ce ta rasu ne misalin ?arfe tara na safiyar Asabar. Kuma a yau Lahadi ake sa ran yin jana’izarta bayan iso da gawarta zuwa Najeriya daga Masar.

Sanarwar da Masarautar Kano ta fitar ta ce Hajiya Maryam Ado Bayero ta rasu tana da shekara 80 a duniya bayan gajeruwar rashin lafiya.

Related posts

Leave a Comment