Kano: An Nada Ganduje Sarautar Jakadan Zaman Lafiya

Kungiyan Makafin Arewacin Najeria, wadanda suka taso daga Jihohi shatara sun hadu A Jihar Kano domin gabatar da Taronsu nagani a Fada

A Jawabin Gwamnan kano Dr,Abdullahi Umar Ganduje yayin Taron, yace Allah yayi Makafi da Baiwar da ba kowa kedashi yakuma ce zasu fito da Hanyoyinda za’a tallafa musu a koya musu Sanao’i domin dogaro da kai, Sannan a yimusu hukamar dake kula da Masu bukata ta Musamman domin saukaka musu al’amura a kusa dasu, Kuma an dauki Nauyin karatun yayansu daga Furaimare har zuwa matakin University kyauta ga Yayansu.
Ganduje yakuma yabawa da irin karamcinda kungiyar ta nuna masa da kuma Jakadancin da Suka bashi

Da yake jawabi Shugaban kungiyar makafi ta kasa reshen Arewacin Najeriya Malam Muntari Saleh, Yace babu shakka Gwamna Dr,Abdullahi Umar Ganduje ya cancanci yabo dubaga irin Gudun mawar da Yake bawa Masu Bukata Ta musamman,Hakanne yasa Sukaga yadace da suyi tarukansu na Tsawon kwanaki uku a jihar kano da kuma yiwa kasa
Addua.

Muntari Sale Ya kara da Cewa, Ganduje yayi musu duk irin abinda suke bukata saidai Sun gabatar masa da sauran bukatun da Sukeso cikin kokarinsa da yayi musu, ciki Harda kafa musu hukumar Da ke kulada masu bukata ta musamman, Da motar da zasu dunga zurga zurga, da karatun yayansu.
Hakan yasa suka zabi nadashi jakadan zaman lafiya

Itama Mai Bawa Gwamna shawara na musamman akan harkokin Kingiyoyi masu zaman kansu
Hajiya Yardada Maikano Bichi, tace Baataba Gwamnati me bada kulawa da harkokin masu Bukata Ta musamman ba irin Gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje
Tace za’a kuma cigaba da fito da Tsare Tsare da dama, dazasu Taimaka wa Masu Bukata Tamusamman

Daga Karshe anyi wassan Nuna fasaha Ta Makafi, Dasuka hardar da Wakoki, Kama kaza, yar buya dasauransu

Labarai Makamanta

Leave a Reply