Kano: An Karrama Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai

Kungiyar mata musulmi reshen jihar Kano sun karrama shugaban hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano Malam Ismail Na’abba Afakallahu inda suka ba shi lambar yabo ta girmamawa.

Hakazalika kungiyar ta baiwa Malam Afakallahu sarautar SARKIN TSAFTACE HARSHE A FAGEN YABON MANZON ALLAH S.A.W

Hakan ba ya rasa nasaba da tsare-tsaren da shugaban hukumar ya kawo na tantance Sha’irai da tace wakoki kafin sakinsu a gari domin kaucewa wuce gona-da-iri da aka jima ana samu, da kuma matakin tsaftace majalisin yabo daga samun tashin-tashinar tashin hankli kamar yadda hakan ya saba faruwa a baya.

Kawo yanzu wannan duk ya zama labari wanda hakan ya karawa gwamnatin Kano kima da daraja daga sassa daba-daban a kasar nan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply