Rahotanni dake shigo mana yanzu daga birnin Kano na bayyana cewar hukumar Yan-sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta kama daya daga cikin manyan Kwamandojin hukumar Hisbah a Jihar Kano da matar Aure a Hotel.
Helkwatar hukumar dake Jihar Kano ta gazgata labarin cewar ofishin Yansanda dake Nomansland, a jihar Kano sun kama wani Jami’in hukumar Hisbah mai suna Sani Nasidi Uba Remo, da matar Aure a wani Hotel a unguwar Sabon gari.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar mijin matar ne ya tseguntawa wani Jami’in Dan sanda bayan yana zargin matar tasa, sai Allah ya temaka suka yi mishi tarko har suka kamashi a Sabon gari da Matar.
Wani rahoton bayan fage ya tabbatar da cewar Abokan Sani Nasidi daga ofishin Hisbah sun yi ta kokarin karbar belin shi, Yan-sanda sun bayar da belin sa tare da gindaya manyan Sharid?u.
Babban Kwamandan hukumar Hisbar a Jihar Kano Sheikh Muhammad Haroun Ibn Sina, ya ce ya sha mamaki tare da ka?uwa bisa ga wannan mummunan Labarin ya kuma yi alkawarin daukar matakin daya dace, har ya na?a kwamitin bincike kuma ya bukaci a bashi cikakken rahoto nan d kwanaki 3.
DIMOKURADIYYA