Kano: An Kafa Kwamitin Bincikar Kwamandan Hisbah Da Aka Kama Da Matar Aure

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kafa kwamitin mutum biyar domin binciken wani kwamandan hukumar mai suna Malam Sani Remo, daya daga cikin manyan jami’an hukumar kan zargin kamashi da matar aure turmi da Ta?arya a Otal.

Kakakin hukumar Hisbah, Lawal Fagge, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba cewa an ba kwamitin kwanaki uku su kammala bincikensu kuma su dawo da bayani. Fagge ya ce bayan an kammala binciken, hukumar za ta dauki matakin da ya dace kan jami’in.

“Amma idan sakamakon binciken ko shawarwarin sun fi karfin hukumar, za’a mika lamarin ga hukumar da ta dace don daukan mataki,”. Yayinda aka tambayesa inda aka ajiye jami’in da ake zargi da laifin, ya ce an sakeshi har zuwa lokacin da za’a kammala binciken saboda ba’a tabbatar ya aikata laifin ba.

Rahotanni sun ce ?an sanda daga ofishin Noman’s Land ne ya kama Malam Sani Rimo a dakin wani otel a yankin Sabon Gari da ke Kano. Majiyoyi daga rundunar yan sanda sun ce sun samu rahotanni ne game da shi sannan suka garzaya suka kama shi tare da matar a dakin.

A baya Malam Rimo shine jami’in tawagar yaki da masu karuwanci na hukumar ta Hisbah wanda karuwai ke shakkarsa sosai a yankin na sabon gari. A halin yanzu shine jami’in da ke kula da sashin masu hana bara a Kano.

Related posts

Leave a Comment