Kano: An Janye Dokar Hana ‘Yan A Daidaita Sahu Hawa Manyan Tituna

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta janye dokar da ta hana ƴan adaidaita-sahu bin wasu manyan tituna cikin kwaryar Kano.

Shugaban Hukumar kula Da Zirga-zirgar Ababen-hawa, KAROTA, Baffa Babba Dan’agundi ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai a Kano.

Ya ce an janye dokar ne saboda matuƙa baburan adaidaita-sahu ɗin sun yi biyayya kuma al’umma sun yi suka a kan dokar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply