Kano: An Iza Keyar AbdulJabbar Zuwa Gidan Yari

Rahotanni da muke samu daga jihar Kano sun tabbatar mana cewa, gwamnati ta kame Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara bisa laifin batanci ga manzon Allah SAW a wuraren karatuttukanshi.

Wata sanarwa da kwamishina na yada labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa hakan ya biyo bayan karbar rahoton farko da aka yi daga ofishin ‘yan sanda daga Ofishin Babban Lauya da kuma kwamishinan shari’a wanda ya shirya tuhuma kan malamin.

KARANTA WANNAN: Dalla-dalla: Bayanin yadda ake cike fom na neman ayyukan gwamnati 3 da ake dauka yanzu Sheik Abduljabbar | Hoto dailytrust.com Source: Facebook Daily Trust ta tattaro

Sanarwar na cewa: Abduljabbar Nasiru Kabara, mazaunin garin Kano ya shahara wajen tafsiri mai rikitarwa da maganganun da ake yi wa kallon na batanci ga sahabbai da kuma yin batanci ga Manzon Allah Muhammad (S.A.W) an gurfanar da shi a gaban kotu saboda laifin batanci.”

“Wannan ci gaban ya biyo bayan karbar Rahoton Bayanai na Farko daga ofishin ‘yan sanda ta Ofishin Babban Lauya kuma kwamishinan shari’a wanda ya shirya tuhumar kan malamin.

“Daga baya an gurfanar da Abduljabbar a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuli a gaban Alkalin Kotun Koli ta Shari’a dake Kofar Kudu, Alkali Ibrahim Sarki Yola, inda aka ambaci tuhume-tuhumen da suka hada da batanci, tayar da hankali, da kuma laifuka daban-daban.

“Bayan zaman kotun, ta dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Yuli, yayin da malamin zai ci gaba da zama a hannun ‘yan sanda har zuwa ranar Litinin lokacin da za a tura shi gidan yari har zuwa ranar da aka dage karar.”

Related posts

Leave a Comment