Kano: An Gurfanar Da Jaruma Amal Umar Gaban Kotu

images (10)

Ana zargin Amal da yunƙurin ba da cin hancin naira dubu 250 ga wani ɗan sanda mai suna ASP Salisu Bujama da ke rundunar ƴansandan, shiyya ta ɗaya da ke Kano.

A cewar mai gabatar da ƙarar, Amal na yunƙurin bayar da cin hancin ne domin hana binciken ƴan sanda kan zargin saurayinta da almundahanar kuɗi.

Lamarin ya bayyana ne lokacin da wani Yusuf Adamu ta hannun lauyansa ya shigar da ƙorafi ga mataimakin babban spetan ƴansanda Umar Mohammad Sanda, inda yake zargin saurayin jarumar da yin sama da faɗi da kuɗin da ya kai naira miliyan 40 da sunan kasuwanci.

Ƙorafin da aka shigar ya sa ƴansanda gudanar da bincike wanda ya gano cewa saurayin jarumar ya tura mata naira miliyan 13 ta asusun bankinta.

Acewar kakakin rundunar ƴansanda shiyya ta ɗaya, CSP Bashir Muhammed, an gayyaci ƴar fim ɗin domin amsa tambayoyi daga bisani kuma aka bayar da belinta sai dai an hana ta fita daga wata mota da ake zargin saurayin nata ne ya siya.

Jarumar ta tabbatar cewa kuɗin da ke cikin asusunta mallakin saurayinta ne duk da ta yi iƙirarin cewa naira miliyan takwas kawai ya tura mata.

Bayan da aka ba ta beli ne kuma ta garzaya babbar kotu a Kano domin neman a dakatar da ƴansanda daga binciken da suke a kanta. Kotun ta hana ci gaba da binciken da ƴansanda ke yi kan jarumar, abin da ya bai wa Amal dama ta yunƙurin ba da toshiyar baki ga ɗansandan da ke binciken ASP Salisu Bujama.

Jami’in ya yi watsi da cin hancin inda kuma ya kamata ta tare da shaidar zargin ba da cin hancin abin da ya sa aka gurfanar da ita gaban kotun majistre ranar Laraba.

Laifin da ake zargin jarumar ta aikata ya saɓa sashe na 118 na dokar penal code wadda ta haramta bai wa jami’in ɗansanda cin hanci.

Labarai Makamanta

Leave a Reply