Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa, Wata babbar kotun shari’ar Musulunci ta karanta wa Shafi’u Abubakar matashin da ake zargi da cinna wa mutane wuta a masallaci tuhume-tuhume guda huɗu da ake yi masa waɗanda suka haɗa da;
- Zargin sanadiyyar kisan mutum 23 da gangan ta hanyar cinna musu wuta a masallaci a garin Gadan wanda aka fi sani da Larabar Abasawa cikin ƙaramar hukumar Gezawa.
- Yunƙurin kisan wasu mutum biyu a ranar 15 ga watan Mayu 2024 a garin Gadan.
- Raunata wasu mutane ta hanyar watsa musu fetur a masallaci lamarin da ya yi sanadin haifar musu da munanan raunika.
- Ƙone masallaci da abubuwan da suke ciki alƙalin kotun Ustaz Halhalatul-khuza’i Zakaria ya tambayi Shafi’u Abubakar wanda ake tuhuma ko ya fahimci tuhumar sai ya amsa da cewa “E” ya fahimta tare da tabbatar da cewa “lalle haka abin yake ya aikata”.
Babbar kotun Shari’ar MusUluncin ta ɗage zamanta zuwa ranar 1 da 2 ga watan gobe na Agustar 2024, inda ake fatan kotun zata yi masa hukuncin kamar yadda masu kara suka nema.