Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani ɗan damfara da ke yaudarar mutane cewa shi aljani, bayan shafe shekara uku yana cinye soyayyun kaji da naman kai na sa da rago da yake sa wani mutum na aika masa.
A wani faifen bidiyo da ya riƙa yawo a shafukan sada zumunta, an ga yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, yana bayyana yadda wani matashi ya kai ƙorafi a ofishin ƴan sanda da ke unguwar Bompai.
Mutumin ya kai ƙorafin ne kan cewa wani aljani ne ya shafe tsawon shekara uku yana kiransa a waya yana tilasta masa ya kai masa kaji soyayyu ko dafaffu, har ma da kan rago da na sa.
DSP Kiyawa ya kuma ce ”Mutumin da ya kai ƙarar ya kuma bayyana cewa aljanin ya riƙa tsoratar da shi cewa muddin bai kai abin da aka umarce shi ya kai ba zai iya mutuwa ko kuma a ƙone masa gida”.
”Hakan ne ya sa kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Habu Ahmed Sani, ya tayar da ƴan sandansa na ‘Operation Puff-Adder’ ƙarƙashin jagorancin CSP Abdulkarim Abdullahi tare da ba su umarnin duk inda wannan aljani yake a kamo shi”, in ji Kiyawa.
Rundunar ƴan sandan jihar Kanon in ji ta bakin CSP Kiyawa, ta samu nasarar cafko wannan mutum da ya riƙa yi wa wadanda ya saba damfara cewa shi aljani ne.
”Bayan mun kamo shi mun samu kayayyaki a tare da shi da suka haɗa da layu, da kudade Dalar Amurka da Nairori duk na bogi, da sauran tarkacen kayayyaki irin na tsubbu”.
A cikin faifen bidiyon ana iya ganin Aliyu Haruna Usman mai shekara 34 wanda ya kai ƙorafin game da wannan aljani yana amsa tambayoyi daga DSP Kiyawa wanda ya nemi ƙarin bayani daga gare shi.
Aliyu wanda ke sanye da wata doguwar riga mai launin ruwan toka da ratsin fari, kuma ya ɗora wata kwat a kai ita ma mai launin ruwan toka, sanye kuma da hula ɗinkin hannu da aka fi sani da ‘Zanna Bukar’ mai launin makuba, ya fara yi masa bayani kan yadda wannan aljani ya shafe shekara uku yana yadararsa.
”Abin da yake faruwa aljanu ne ke kira na a waya suna fada min lallai-lallai ga abin da zan yi musu a rayuwa, idan kuma na ƙi abubuwa biyu zuwa uku za su iya faruwa da ni.
“Suka tayar min da hankali kwata-kwata a rayuwata – aka fahimci gaskiya a yanayin da nake ciki ina buƙatar taimako”.
”Cikin ikon Allah aka yi gamo da katar suka ba ni kuɗi na bogi, ni kuma na ɗauka ka kawo wa rundunar ƴan sanda, na kuma haɗa musu da lambar wannan aljani da yake kira na, kuma suka yi bincike Allah ya ba su iko da nasarar kama wannan aljani,” in ji Aliyu.
Aliyu ya kuma bayyana cewa su kan buƙaci ya riƙa kai musu abubuwa da dama.
”Akalla na kan ba su kaji, da wuyan sa, da nono ƙwarya ɗaya da na kan saya lokuta-lokuta; an ai shekara uku ina yi musu wannan hidima, amma yanzu gaskiya na ga cewa ba zan iya ba, shi yasa na ce bari in kai gaban mahukunta.”
Rundunar ‘yan sandan wacce ta riga ta cafke wannan mutum da ke ikirarin cewa shi aljani ne, wanda ya bayyana mata cewa sunansa Umar kuma shekarunsa 28, yana kuma zaune ne a unguwar Badawa.
Ya ce shi da ya ce shi dan asalin garin Gashua ne a jihar Yobe.
An dai nuno shi sanye da wata koriyar rigar sanyi jaket mai hade da hula da gashi-gashi a wajen wuyan, yayin da jami’in hulɗa ta jama’a na rundunar ƴan sandan ya umarce shi da ya saɓule hular ta koma gadon bayansa kafin ya fara amsa tambayoyin da aka yi masa.
”Karya yake yi kawai so yake yi a yi masa kudi, ya ce yana so ya kai kamar ‘Mudassir and Brothers’ sannan kuma ya yi abubuwa kala-kala domin ya yi kuɗin nan”, inji Umar aljani.
Ya kuma kara da cewa ”Sannan kuma ya ce ya yi abubuwa kala-kala – gaskiya wadansu abubuwan ba na so in fada da bakina.
A faifen bidiyon dai an nuno wasu tarkacen kayayyaki na tsubbu da suka hada da wata ƙwarya da a cikinta aka rubuce ta da wani hatimi da Larabci, da farin ƙyalle, da takardu da turaruka, da wasu kwalabe da gwangwanaye da ba a nuna abin da suka ƙunsa ba.
Akwai kuɗaɗe damin dalar Amurka da nairar Najeriya da Umar aljani ya shaida wa ‘yan sanda cewa duk na bogi ne.
”Wannan kudin da kuka gani na Aliyu ne, kuma yana da wasu tari a gida an yi masa wasu duk na bogi har a Nijar haka ya fada min,” Umar ya sake shaida wa ‘yan sanda.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce yanzu haka ta duƙufa kan bincken ganin cewa sun bi diddigin waɗannan kuɗaɗe da yadda aka buga da kuma shigo da su Kano ko kuma Najeriyar.