Kano: Adadin Daliban Islamiyya Da Ruwa Ya Ci Ya Doshi 50

Rahotanni dake shigo mana daga Karamar hukumar ?agwai ta jihar Kano na bayyana cewar an gano gawawwakin mutane 13 da ba a san inda suke ba tun bayan hadarin jirgin ruwan da ya auku a wani kauye a garin Bagwai, jihar Kano.

An ruwaito cewa an gano gawarwarkin mutane 13 da suke nutse a hadarin ruwa. Hakan ya na nufin adadin mutanen da ruwan ya ci a mummunan hadarin da aka yi ya kai 42.

Ana sa ran a safiyar ranar Talata ayi jana’izar wadanda suka riga mu gidan gaskiya a kauyen Badau, kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Idan ba a manta ba, jirgin ruwa ya kife da mutane kusan 50 da suka taso daga makarantar Madinatul Islamiyya daga wani kauye, za su je Bagwai Wadannan yaran makaranta sun taso ne daga bikin Mauludin Annabi Muhammadu (SAW).

Ba wannan ne karon farko da jirgi ya kife a wannan ruwa ba. An gano gawar mutane 29, daga ciki an tabbatar da cewa an ceci mutane bakwai da suka yi rai.

Rahoton yace gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki abin da ya jawo wannan hadari da ya yi sanadiyyar mutuwar ?aliban islamiyya da dama.

Baya ga haka, Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya raba motoci biyu da za su rika safarar fasinjoji daga kauyen Badau zuwa garin Bagwai.

Sannan gwamnati ta raba buhunan masara da shinkafa da kuma sukari da gishiri ga wadanda abin ya shafa, baya ga gudumuwar kudi Naira miliyan shida.

Related posts

Leave a Comment