Kano: Abba Gida-Gida Zai Bar Tafiyar Kwankwasiyya

Wata majiya daga jihar Kano ta bayyana cewa Abba Kabir Yusuf na shirin barin tafiyar ta Kwankwasiyya ne bayan da ya fahimci cewa, Jagorar Kwankwasiyya tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr Rabi’u Musa Kwankwaso, na shirin maye gurbin shi da wani ɗan takara a shekarar 2023.

Rahotanni daga birnin Kano sun tabbatar da cewa za a maye gurbin Abba Gida-Gida ne da tsohon shugaban hukumar tallafin kudaden jami’o’i, AB Baffa a matsayin dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Alhaji Kabiru Yusuf wato Abba Gida-Gida wanda suruki ne ga Kwankwaso shi ya tsayawa jam’iyyar PDP takarar Gwamna a Jihar Kano a zaben Shekarar 2019, inda suka fafata da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Zaɓen Gwamnan jihar Kano na shekarar 2019 ya zo da wasu abubuwa muhimmai, jam’iyyar PDP ta yi rawar gani sosai, amma bisa ga jajircewa ta ɓangaren Gwamnatin Ganduje ya sanya jam’iyya mai mulki ta APC samun nasara.

Ana ganin idan har ficewar Abba Gida-Gida a tafiyar Kwankwasiyya ta tabbata, da alamu jam’iyyar PDP a Kano zata iya samun rauni a zaɓen Gwamna da za’a yi a shekarar 2023.

Labarai Makamanta