Kamfanin Facebook Ya Sauya Suna Zuwa Meta

Facebook ya sauya sunan kamfanin zuwa Meta a wani gagarumin garanbawul.

Kamfanin ya ce ya “fa?a?a ayyukansa” ta yadda kamfanin zai ?unshi dukkan abubuwan da yake yi, saboda yana abubuwan da suka zarta shafukan sada zumunta zuwa yin abubuwa na kamar gaske wato virtual reality.

Sauyin bai shafi shafukan kamfanin ba kamar su Facebook da Instagram da Whatsapp, kawai sunan babban kamfanin da ke da mallakinsu ne ya sauya.

Matakin ya biyo bayan wasu jerin labarai marassa da?i ne a kan kamfanin, kan wasu bayanai da wata tsohuwar ma’aikaciyarsu ta saki.

Frances Haugen ta zargi kamfanin da fifita riba a kan tsaron mutane.

A shekarar 2015, Google ya yi wani sauyi a kan kamfaninsa inda ya mayar da sunan Alphabet, sai dai har yanzu ba a saba da sunan ba.

Related posts

Leave a Comment