Kamfanin Dangote Zai Samu Sama Da Miliyan Dubu Talatin A Karshen Shekara

Shugaban rukunin kamfanin Dangote, kuma mutumin da ya fi kowa ku?i a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa zuwa ?arshen shekarar nan ta 2024, yana sa ran jimillar ku?in da zai ri?a samu a harkokin kasuwancinsa ya kai sama da dala miliyan dubu 30.

A wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta CNN, hamsha?in attajirin ya ce cimma wannan buri zai sa kuma kamfanin ya kasance ?aya daga cikin manya-manyan kamfanoni 120 na duniya.

Attajirin ya ce, yadda ya sauya fasalin kamfanin ta yadda manyan jami’ai ke jagorantar muhimman ?angarori na harkokin kasuwancin nasa, cimma wannan buri na samun dala biliyan 30 zuwa ?arshen shekarar ba abu ne da zai zama mai wahala ba.
“Mun raba kamfanin gida biyu a yanzu. Ni ina matsayin shugaban rukunin, sannan kuma akwai shugabannin rukunin na ?angaren mai da iskar gas, sai kuma shugaban rukunin sauran harkokin kasuwancin,” in ji shi.
Ya ?ara da cewa, ”duka wa?annan idan ka ha?a su, zuwa ?arshen shekarar nan, za mu samu rukunin kamafanin da zai samu dala biliyan 30, kuma wannan babban abu ne. Hakan na nufin za mu kasance cikin manyan kamfanonin duniya 120.’

Related posts

Leave a Comment