Babban Shugaban Kamfanin na ATAR mallakan Gidan Rediyo da Talabijin na Liberty Alhaji Dr. Ahmed Tijjani Ramalan ya bayyana hakan, inda yace dukkanin shirye shirye sun kammala na kaddamar da tashoshin a biranen Kano da Dubai na haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Sabbin tashoshin na Rediyo dake kan mita 103.3 FM Kano, da Black Entertainment Studios da ke Dubai, babbar manufar buɗe wadannan tashoshin shine domin kara inganta shirye shirye cikin harshen Hausa da ingantattun labarai, al’amurra yau da kullum Siyasa a tashar Rediyo ta Kano FM, da shirye-shirye na tarihi da fadakarwa a tashar Black Entertainment a yankin gabas ta tsakiya.
Sabbin tashoshin na Kano da Dubai an gina su ne bisa tsarin tashar Liberty Rediyo da Talabijin na Liberty, wanda ke da manufar ilimantar da jama’a a duniya baki ɗaya.
Ramalan ya ƙara da cewar babu gudu babu kuma ja da baya a kokarin da kamfanin na ATAR ke yi, na fadakarwa gami da ilimantar da jama’a, ta hanyar kwararrun ma’aikata da kayayyakin aiki na zamani.
Ana sa ran tashoshin zasu fara gwajin shirye-shiryen su a cikin wannan wata na Ramadan, yayin da shirye-shirye na kasuwanci ake sa ran fara su a cikin watan Mayu da Yunin wannan shekara ta 2021.