A wani bincike da jaridar Daily Trust ta gabatar, ya bayyana yadda cutar Coronavirus ke hauhawa kamar farashi a cikin sabuwar shekarar nan.
Kididdiga daga hukumar kula da ya?uwar cutuka ta Nijeriya NCDC ta bayyana cewa cutar Covid-19 ta yi silar ajalin mutum 193 a cikin kwanaki 20 daga 4 ga watan Janairu zuwa 24 na wannan shekarar da muke ciki.
Ya zuwa Larabar da ta gabata jimillar wadanda suka harbu da cutar ya kai 126,160 da sabbin harbuwa 24,251 yayinda ta kashe 1,544.
A satin da ya gabata ne dai shugaba Buhari ya sa hannu kan dokar cutar don ganin an dakile yaduwarta cikin al’umma, kuma duk wanda aka samu da karya dokar zai fuskanci tara ko zaman gidan yari na tsawon wata 6.
Da yake jawabi yayin zantawa kan lamarin, Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban kasa na yaki da Covid-19 Boss Mustapha ya bayyana cewa tuni masana sun dukufa don shawo kan matsalar cutar.