Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC a zaben 2023, Omoyele Sowore, ya yi martani a kan tuhume-tuhumen da ake yi wa dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele Sowore ya bayyana zarge-zargen a matsayin shirme da yaudara don ara wa masu rike da madafun iko a gwamnati lokaci Ya ce ainahin laifin da Emefiele ya aikata zai kai tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, danginsa da surukansa kasa.
Sowore, ya dasa ayar tambaya kan yanayin yadda hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ke tafiyar da lamarin dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele. A wata wallafa da ya yi a shafin Twitter a ranar Asabar, Sowore ya yi martani a kan tuhume-tuhume biyu da gwmanatin tarayya ke yi wa Emefiele na mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Ɗan fafutukar ya bayyana cewa tuhume-tuhumen da ake yi wa Emefiele duk kokari ne na siyan lokaci ga mutanen da ya yi zargin hukumar DSS na karewa. Sowore ya ambaci abokan harkallar Sowore Ga wallafarsa wadanda suka haɗa da gwamnoni da ministoci da wasu ɓangare na iyalan tsohon shugaban kasa Buhari.