FIM: Rahama, me ya ja hankalin ki ka ka shigo harkar fim?
RAHAMA A. IBRAHIM: To, da man dai tun farko ni ba Musulma ba ce, ni Kirista ce kuma ana kira na da Judith A. Ibrahim. Na taso a gidan malamai na addinin Kiristanci. To haka dai Allah ya sa mun son kallon finafinan Hausa har ta kai ga ina kllon wasu finafinan da su ke fito da kyawawan ?abi’un Musulunci. Ta hanyar haka ne kuma su ka ba ni sha’awa har na ji ina ?aunar na shiga Musulunci har ma na yi sha’awar shigowa ita karan kan ta masana’antar domin in fa?i abin da addinin ya yi min.
FIM: Tun tsawon wane lokaci ne ki ka shiga Musulunci sannan kuma wane irin ?alubale ki ka samu tsakanin ki da iyayen ki ko ‘yan’uwan ki?
RAHAMA: Kusan shekara ta ta uku kenan da shiga wannan addinin na Musulunci.Na gamu da matsaloli ko in ce ?alubale da dama daga wurin ‘yan’uwa na har ma da mahaifiya ta wadda a da ta daina yi mani magana; ko na yi mata magana ba ta mayar min. Sannan su kuma ‘yan’uwa na su ka tsane ni tare da ?o?arin kai ni wajen da ake yin hukunci wanda da a ce an samu nasarar yi mani hukunci kan wannan abu da na yi na barin addinin mu da tuni an juya mini tunani ko kuma an kulle ni, ba wanda zai san yadda na ke. Cikin taimakon Allah da taimakon mahaifiya ta, na tsallake wannan tarkon.
Duk da cewa mahaifiya ta ta yi fushi da ni lokacin da na shiga Musulunci, amma gaskiya daga baya ita ce wacce ta dinga ba ni kariya a duk lokacin da aka yi yun?urin zuwa a kama ni, wanda mu ka yi ta haka har na tsawon shekara ?aya, kafin daga bisani na samu wata dama na gudu daga garin, na zo nan Kano.
FIM: Lokacin da ki ka zo Kano da zummar za ki shiga wannan masana’anta ta Kannywood, da man kin san wani ne a nan ko kuma ku na da wasu ‘yan’uwa haka?
RAHAMA: Gaskiya ni ban san kowa ba a Kano, kawai dai na zo ne ina lalube wanda har ta kai ni zuwa yanzu. Amma kuma fa ba na iya sati biyu ban je gidan mu ba na ga mama na, domin abin da ban fa?a ba shi ne baba na Allah ya yi masa rasuwa tun ina yarinya.
FIM: A matsayin ki na ba?uwa a wannan masana’anta, wane irin ?alubale ki ka samu da jarumai da masu shirya finafinai?
RAHAMA: Gaskiya na sha fama da wahala sosai, saboda na fuskanci ?alubale da dama. Na fa?a hannun mutanen da gaskiya ba su da imani, amma daga ?arshe Allah ya ha?a ni a hannun wa?anda su ka taimaka min kuma su ka ?auke ni har kawo wannan matakin a yanzu. Na ha?u da wasu daraktoci wa?anda na same su a kan zan shiga wannan harka ta fim, na yi zaton cewa darakta shi ne sama da kowa, wanda ni ban san yadda karatun ya ke ba, a inda wasu su ka guje ni, wasu kuma ba su kar?e ni ba har ma da wa?anda su ka cuce ni ma, don na bada ku?i bila adadin.
FIM: Zuwa yanzu a tsawon shekara biyu da ki ka yi a wannan masana’anta, finafinan ki nawa?
RAHAMA: Bayan da na shigo har na samu wa?anda su ka kar?e nI da hannu biyu-biyu tare da yi mani wani fim, kuma ikon Allah fim ?in ya na tafiya ana kuma kallon sa. Wasu kuma finafinan da na yi akwai irin su ‘Tawagar ‘Yan Mata’ da ‘Bautar Zuciya’, da dai sauran su da ba zan iya lissafawa ba.
FIM: Tsawon wane lokaci ki ka ?auka a garin ku kafin ki dawo nan Kano?
RAHAMA: Gaskiya a lokacin da na shiga addinin Musulunci ba a nan take na bar garin mu ba, amma ban samu ?ofar fita ba saboda ba hali domin an sa masu sa ido a kai na. Sannan da na ?an samu ?ofa sai na fito na bar garin na dawo Kano. Kuma ba zan iya sati ban ga mahaifiya ta ba gaskiya saboda ba zan iya rayuwa ba in ba ita.
FIM: Wane buri ki ke da shi a wannan masana’anta ?
RAHAMA: Burin da na ke so na cimma a cikin wannan masana’anta gaskiya bai da yawa ko ma in ce guda ?aya ne: tunda ni fim ne gata na, wato shi ne dalilin da ya zamto silar shiga ta addinin Musulunci, shi ne na ga wani ma mai irin tunani irin nawa shi ma zai iya zuwa ya kar?i Musulunci domin shi ma ya samu dama.
FIM: Ya batun aure kuma?
RAHAMA: To, aure sai Allah ya kawo miji saboda ana cikin wani yanayi, dole sai ka samu miji nagari wanda ya san addini da tarbiyya, ba kuma zai tsangwame ka ba, tunda ni ka ga ban san addinin Musulunci sosai ba. To kuma a yadda na ke gani a ma?wabta aure sati ?aya ko biyu ya mutu, to shi ne kawai tsoro na gaskiya.
FIM: Da me za ki ?ar?are wannan tattaunawar tamu?
RAHAMA: Kira zan yi ga ‘yan masana’antar nan mu koyi ha?in kai, kuma ina ro?on Allah ya ?ara ha?a mana kan mu baki ?aya.
Sannan akwai wasu ?ananan masifu da su ke tasowa, dole sai an yi ha?uri, sai da yawaita addu’a da ri?e Allah.