Kai Abin Zargi Ne Muddin Ba Ka Fallasa Masu Satar Dalibai Ba – ACF Ga Matawalle

Kungiyar tuntuba ta Dattawan Arewa, ACF ta bayyana cewa Gwamna Matawalle ya fito ya bayyana sunayen wanda yace ya sani da suka sace daliban makarantar Jangebe.

Gwamna Matawalle a lokacin da Sarakunan Jihar Zamfara suka kai masa ziyarar jaje kan satar daliban, ya bayyana cewa idan ya fadi sunan wanda suka sace daliban, ‘yan Najeriya zasu sha Mamaki.

Sannan kuma ya bayyana cewa wasu sun baiwa ‘yan Bindigar kudi dan kada su saki daliban.

A martaninta, ACF ta bakin shugabanta, Audu Ogbe a sanarwar da kakakin, Emmanuel Yawe ya fitar tace gwamnan ya fito ya fadi sunan wanda suka sace daliban, in kuma ba haka ba, Jami’an tsaro su tuhume shi da hannu a lamarin.

Kungiyar tace kalaman na Gwamnan sun basu kunya dama yankin Arewa gaba daya.

Related posts

Leave a Comment