Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi ikirarin cewa tsaro yanzu ya tabbata a titin Abuja zuwa Kaduna, sai dai kawai fargabar wata matsala ta daban.
El-Rufai ya kara da cewa ganin yadda Korona ke cigaba da yaduwa a kasar nan, dole sai an kiyaye dokar hana yaduwar ta a koda yaushe.
Wannan tsari na jirgin kasa zai taimaka wajen dakile yaduwar Korona.
Maganan rashin tsaro kowa a titin Abuja zuwa Kaduna kusan babu shi ne yanzu domin rabon da ace anyi garkuwa da wani a titin Abuja tun a Oktoban bara.
El-Rufai ya zayyano wasu dokoki da matafiya za su tabbata sun kiyaye a lokacin shiga jirgi kamar haka, ” Dole mai shiga wato fasinja ya saka takunkumin fuska a lokacin da ya iso tashar jirgin sannan za barshi a fuska har sai ya sauka.
Da yake tsokaci game da karin kudin jirgin da hukumar Jiragen kasa ta yi El-Rufai ya ce shi bai ga wani abin tashin hankali a kai ba.
” Ni fa a gaskiya karin kudin ma yayi min kadan ne da an sa shi ya fi yadda aka saka a baya saboda, sai kazo tashar ma baka samu tikiti ba, sai ta bayan fage. Kuma a bayan fagen sai yadda suka yi da akai.
” Wannan kari zai sa masu yi harkallar tikitin su daina. Wannan shine ya fi dace. Amma karin kudin jirgi kam yayi daidai.
” Maimakon ace wasu ne ke harkallar tikitin gara gwamnati ta kara kudin don ta amfana da shi.
Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana cewa sufurin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja zai dawo aiki daga hutun Korona, ranar 29 ga Yuli.
Minista Amaechi ya ce an kara kudin kujerar jirgi a dalilin canja fasalin zama domin bin dokar bada tazara a tsakanin mutane.
Kujerar da ake biyan naira 1300 ya koma naira 3000, kujerar naira 2500 ya koma naira 6000.
Amaechi ya ce sai da akayi tattaunawa mai zurfi, har da shugaba Buhari kafin a cimma wannan matsaya.
Bayan haka an kawo sabbin tarago domin fasinjoji.
” Za a zo da taragon dake daukan mutum 24, 56, 68, da mai daukan 88.
” Mutum zai zabi wanda yake so kuma kowannen su kudi sa da ban ne. Sannan muna kokarin ganin jirgin yay sawu 14 a rana maimakon 8 da yake yi a da.” Inji shugaban Hukumar Jiragen Sama ta Kasa, Mr Okhiria.
Okhiria ya kara da cewa nan da watanni uku za a fara saida tikitin kujeran jirgin ta yanar Gizo.