Kaduna: Zakzaky Zai Sake Gurfana Gaban Ƙuliya A Yau

A yau Juma‘a ne kotun Kaduna za ta saurari shari‘ar da ake yi tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da Zakzaky wanda ake tsare da shi tsawon shekaru tun bayan artabun da aka yi a Zariya na shekarar 2015, tsakanin Sojoji da ‘Yan Shi’a.

A bayan an sanya ranar Alhamis 30/07/2020 ne domin sauraren karar sai ranar ta zama ranar hutun Babban Sallah ne, inda lauyan Zakzaky ya bayyana hakan a matsayin wata manakisa; “Sunyi ‘declaring public holiday’ yau da gobe, watakila saboda kawo cikas a case din, sai zuwa litinin za a sa wata ranar” inji lauyan.

Lauya Femi Falana, shi ne babban lauya mai kare Zakzaky, ya nemi alkalin kotun da kotun da yayi watsi da shari’ar saboda rashin wata gamshashiyar jujja na cigaba da tsare Zakzaky din sama da shekaru Biyar batare da wani dalili ba.

Tun watan Fabrairu na wannan shekarar ba’a sake zaman ba a ranar 6 da kuma 25 na wata, sakamakon tafiya hutun bai 1 da aka tafi sakamakon cutar Annoban Corona, kimanin watanni 5 kenan baya.

Zakzaky yana fama da munanan raunuka da suka hada da lalacewar ido daya, tare da zaman barbashin harsashai cikin kwakwalwar sa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply