Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin Mai girma Nasir Ahmed El-Rufai za ta rusa gidaje da dama a garin Zariya. Kamar yadda muka samu labari, gwamnati za ta rusa gidaje da gine-ginen al’umma a unguwar da ake kira Graceland da ke karamar hukumar Sabon Gari.
Wannan unguwa tayi makwabtaka da makarantar koyon tukin jirgin sama da ke hanyar Samaru, ana zargin filayen unguwar sun shiga cikin filin makarantar.
Gwamna Nasir El-Rufai yana zargin dubunnan mutanen da ke wannan yanki da mallakar filaye ba tare da sun bi ka’idojin mallaka ba.
Mun samu labarin cewa mutane suna ta kuka a kan wannan mataki da gwamnati ta dauka, inda aka baza jami’an tsaro da nufin a rusa unguwar.
Wani mai unguwa a yankin Graceland, Gunji Makama ya shaida wa manema labarai cewa abin da gwamnan Kaduna yake kokarin yi, ya ci karo da dokar kasa. Gunji Makama yace mazauna unguwar sun mallaki takardu kafin su gina gidajen da suke ciki.
Mutanen garin Zaria sun tabbatar mana da cewa an baza manyan motoci da ke tunbuke gine-gine a unguwar Graceland, ana jiran a fara ruguza gidajen jama’a.
Wata majiya ta shaida mana cewa babu abin da zai hana gwamnatin jihar rusa gidajen sai ikon Allah. Motocin jami’an tsaro sun cika gari domin hana rikici.
Ana tunani mutane 200, 000 za su rasa matsuguni idan aka rusa wadannan gidaje da adadinsa ya kai 10, 000 a wannan unguwa da ke garin Zaria.