Kaduna: Za A Ɗauki Ma’aikata Dubu 23 Ayyuka Na Musamman

Gwamnatin jihar Kaduna ta fara sanya matasa maza da mata guda 23,000 a cikin shirin nan na Gwamnatin Tarayya na musamman (SPW).

SPW wani shirin Korona ne na tallafi wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dashi, wanda a cikin shirin mutane 1,000 zasuyi aiki daga kowacce karamar hukuma 774 da ake dasu a kasar.
Ana sa ran wannan shirin zai fara aiki a ranar 1 ga Oktoba, 2020. Kowane daya daga cikin matasan za a biya shi dubu ashirin N20,000 kowane wata.

Da take jawabi yayin bikin kaddamar da shirin a Fatika da ke karamar hukumar Giwa a jihar, shugabar kwamitin zartarwar jihar kuma kwamishina mai kula da aiyukkan jama’a da ci gaban al’umma, Hajiya Hafsat Baba, ta bayyana cewa an tsara wannan shirin ne don magance gibin rashin aikin yi a tsakanin ‘yan Najeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply