Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa ‘yan ta’adda masu Garkuwa da mutane sunkai hari jiya asabar a unguwar Danhoni, dake cikin Karamar hukumar Chikun Jihar Kaduna Sunyi awon gaba da yan jaridu 2 da iyalansu.
‘yan jaridar sune Abdulgafar Alabelewe Na jaridar ( The Nation) da Abduraheem Aaodu na jaridar The Nation da (Blueprint) anyi Garkuwa da su a Daren Asabar a cikin gidajensu.
Alabelewe shine shugaban kungiyar wakilan kafafen yada labarai na kasa reshen Jihar Kaduna, an sace shi ne tare da matarsa da yaransa Guda Biyu, yayin da Abdulrahim Aaodu Wanda shime an sace shi tare matarsa aka bar yarinyarsa wadda akace bata da lafiya.
Daya daga cikin iyalan wadanda aka sacen Taofeeq Olayemi ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun shigo unguwar da misalin karfe na Goma da rabi na dare (10:30pm) suka rinka harbin mai uwa da wabi daga bisani suka balla kofofi da tagogi gidan
Olayemi yace tunda farko yan ta’addan sun tsallaka gidan Abdulgafar inda suka wuce kaitsaye dakinsa sukai awon gaba dashi da matarsa da yayansa guda uku da bakuwa guda daya Wanda daga bisani suka sako bakuwar da yarinya daya cikin ‘ya’yansa sannan suka balle kofar Dakin Aaodu suka dauke shi da matarsa sukabar yarinyarsa wadda bata da lafiya.
Kokafin jami’an ‘ yan sakai su zo maharan sun gudu kuma har izuwa hada wannan rahoton ba kiran waya daga yan’taddan.