‘Yan Ta’adda Sun Kwashe ‘Yan Matan Makarantar Prince Academy Dake Kaduna
Yanzu haka ‘yan ta’adda sun kwashe ‘yan matan makarantar Prince Academy dake karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna a daidai lokacin da suke rubuta jarabawar karshe (WAEC).
Su dai wadannan ‘yan ta’adda sun je garin Chikun ne akan babura sama da dari, inda suka ratsa garuruwa daban-daban kafin su isa garin Chikun.
Lamarin tsaro na ƙara shiga cikin wani mawuyacin hali a jihar Kaduna, tun bayan da ‘yan Bindiga suka juyo da harkokin su jihar a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya jefa jihar cikin wani hali na zaman ɗar ɗar.
A cikin wannan makon ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’adu Abubakar ya ziyarci Gwamna El Rufa’i domin tattauna hanya da mafitar da za’a samu akan harkar tsaro.