Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutane 21

Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun sace mutum 21 a kauyen Udawa da ke karamar hukumar Chikum, da ke jihar Kaduna. Daga cikin wadanda aka sace akwai ‘yan gida daya mutum 17.

Lamarin ya afku ne a wasu tagwayen hare-hare da ‘yan bindigar suka kai a karshen mako, inda 17 daga cikin mutanen da aka sace suka kasance yan gida daya. Malam Hussaini, wani jigo a kauyen Udawa wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce wasu ‘yan bindiga ne suka mamaye yankin sannan suka dinga harbi ba kakkautawa, inda suka raunana mutane da dama.

A cewar Hussaini, an yi garkuwa da mutum hudu a ranar Juma’a, yayin da aka sace sauran 17 din a jiya Asabar a hanyarsu ta zuwa gona da sanyin safiya. Zuwa yanzu dai babu wani bayani daga hukumomi, sannan su ma masu garkuwa ba a ji daga garesu ba.

Labarai Makamanta