‘Yan Bindiga masu garkuwa da mutane a ranar Alhamis sun dawo kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna inda ake zargin su da kwashe matafiyan da ba a san yawansu ba.
Al’amarin garkuwa da mutane a kan babbar hanyar ya yi kasa tun bayan da aka haramta yawo tsakanin jiha da jiha sakamakon barkewar annobar korona a kasar nan. Ganau ba jiyau ba, ya sanar da jaridar Daily Nigerian cewa, al’amarin ya faru ne a kusa da kauyen Katari mintoci kadan bayan karfe tara na safiyar Alhamis. Mohammed Lawan, wanda ya tsallake rijiya da baya sakamakon harin, ya sanar da jaridar Daily Nigerian cewa masu garkuwa da mutanen sun tsare matafiya masu zuwa Kaduna wurin karfe 8:50 na safe.
“Bamu wuce nisan mita 250 a tsakaninmu ba lokacin da muka juya saboda mun hango su.
Na ga mota kirar Honda CRV 98 da kofofinta a bude kuma babu kowa. “Hakan yana nuna sun kwashe mutanen da ke cikinta ne inda suka yi cikin daji. “A lokacin sai muka ji kararrakin harbin bindiga yayin da jirgin sama na sojojin ya iso yankin,” Lawan yace. Har a halin yanzu dai ‘yan sanda basu yi martani a kan aukuwar lamarin ba.