?an bindiga da suka sace ?aliban jami’ar Greenfield a Jihar Kaduna sun sake kashe biyu daga cikin ?aliban, bayan ukun da suka harbe a kwanakin baya, ya zamana yanzu sun kashe biyar kenan.
Cikin sanarwar da kwamishinan lamurran tsaro Samuel Aruwan ya fitar ya ce an tsinci gawar ?aliban ne a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce “Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai tana bakin cikin wannan mummunar aiki da aka yi wa ?aliban da ba su ji ba ba su gani ba da aka sace yayin da suke ci gaba da neman iliminsu don samun makoma mai kyau.”
A makon da ya gabata ?an bindigar suka kashe uku daga cikin ?aliban wa?anda ?an bindiga suka sace a ranar Tatalar da ta gabata.