Wasu ‘Yan Bindiga da ba’a san ko su wanene ba ?auke da manyan makamai sun sace babban Paston Majami’ar
‘Pentecostal Fellowship’ dake jihar Kaduna Pastor Emmanuel Bako da matar sa Sandra.
‘Yan Bindigar sun tarke fasto Emmanuel da Matarsa Sandra a filin taro da addu’o’in musamman na Kirsimeti mai suna Albarka camp, Fadan Kagoma, kusa da Kafanchan karamar hukumar Jema’a.
Kakakin rundunar’yan sandan Kaduna Mohammed Jalige ya tabbatar da wannan al’amari, sannan ya kara da cewa ‘Yan Bindigar sun afka wa filin taron ne da wajen karfe 8:30 na dare, ranar Kirsimeti.
Bayan Pastor Emmanuel da matarsa Sandara, akwai wani mutum daya da ‘yan Bindigar suka arce da shi.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da aukuwar haka.
Ya ce jami’an tsaro ne suka fatattaki ‘yan Bindigar sai dai Allah bai basu sa’an cimma musu ba har suka gudu.
Jihar Kaduna ta yi kaurin suna wajen hare-haren ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.