Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane A Giwa

Rahotanni daga Jihar Kaduna, sun tabbatar da cewa an addabi yankin Giwa da garkuwa da mutane, inda a ‘yan kwanakin nan a ka yi garkuwa da mutane da dama a cikin garin Shika.

Daga cikin wadanda a ka sace har da wata yarinya da ta zo domin yin ta’aziyya a daidai lokacin da a ke fama da kashe-kashe a yankin Kudancin Kaduna, mutanen Karamar Hukumar Giwa suna kukan kan yadda a ke garkuwa da mutane. Majiyarmu ta samu labarin irin satar mutanen da a ke yi a yankin Giwa, ana tsare Bayin Allah har sai ‘yanuwa ko abokansu sun biya kudin fansa.

A ranar 11 ga watan Agustan nan ne masu garkuwa da mutane su ka shiga wani kauye da a ke kira Tashar Zomo, a garin Shika, su ka sace mutane hudu. Wani Bawan Allah mazaunin wannan yanki ya shaidawa majiyarmu cewa har yanzu wadannan mutane da a ka sace, su na hannun ‘yan bindiga.

A lokacin da a ke kukan wannan lamari kuma sai a ka ji ‘yan bindigar sun afka wa garin Tawatsu, sun sace ‘yar wani Bawan Allah a ranar Larabar da ta wuce. Majiyar ta ce wannan yarinya da a ka yi garkuwa da ita, ta zo garin ne daga Jihar Kano domin yi wa ‘yanuwanta ta’aziyyar rasuwa da a ka yi masu kwanakin baya. Har ila yau, a karshen makon da ya gabata a ka wayi gari a garin Shika da mummunan labarin sace wasu mutum biyu.

An yi wannan ne a unguwar Hayin Madaki. Duk wannan abu ya afku ne a Karamar Hukumar Giwa Ta Kaduna, a cikin Kasa da makonni biyu. Tun ba yau ba ana fama da matsalar rashin tsaro a yankin mai iyaka da Katsina. Wani Bawan Allah da ke zaune a Karamar Hukumar Giwa, ya shaida mana cewa satar mutanen da a ke yi a Shika da kewaye ya jefa al’ummar cikin wani yankin cikin halin firgici.

Labarai Makamanta

Leave a Reply