?aya daga cikin wanda ake ta nema cikin mutane uku da ‘yan bindiga suka budewa wuta a garin rigasa dake karamar hukumar igabin jihar Kaduna mai suna Sani Khalil Rigasa an fara samun duriyar sa biyo bayan kirar da masu garkuwa da mutanen sukai wa a iyalan sa da ranar yau.
Idan ba a manta ba, jaridar muryar yanci ta kawo maku ruhoton yadda yan bindiga suka budewa matasan wuta a daren jiya a hanyar titin jirgin kasa dake Rigasa.
Harin yayi sanadiyyar wani matashi Auwal Rabiu mai kimanin shekaru 30. Shi kuma mallam Umar Elkhaddab ya samu rauni a kafafuwan sa na dama sakamakon harbin bindiga.
A ruhoton da muka kawo maku dazu mun shaida maku cewar shi sani Khalil ba ama san a halin da yake ciki ba domin lanbobin wayarsa duk basa zuwa.
Duk da dai yan bindigar basu bayyana kudaden da suke bukata domin fansa ba, Amman hakan yakara kwantar da hankalin iyalan sa da makusanta domin sanin halin da yake ciki.
Matsalar tsaro musamman garkuwa da mutane na daya daga cikin matsalolin da ya addabi yankin arewacin kasar nan inda a koda yaushe al’ummar yankin ke ganin gazawar gwamnati kan shawo karshen wannan matsala.