A cigaba da kai hare haren ta’addanci da ‘yan Bindiga ke yi a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, a yammacin jiya wasu ‘yan Bindiga da ake kyautata zaton Fulani ?auke da muggan makamai sun kaddamar da hari a yankin ?aramar Hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
Harin ya yi sanadin rasa rayukan wasu mazauna kauyukan Bakin kogi da Narido dake yankin ?aramar Hukumar, da jikkata wasu adadi masu yawa gami da salwanta na tarin dukiyoyin jama’a.
Dakarun sojin rundunar Operation Safe Haven sun sanar da gwamnatin jihar kaduna batun wannan hari a ranar Talata, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Kwamishinan tsaron Jihar Samuel Aruwan ya ce dakarun sojin sun gaggauta zuwa bayan kiran gaggawan da suka samu.
Sun isa wurin inda suka tara da mutum biyu, Musa Garba da Yakubu Yawo a mace bayan ‘yan bindigan sun dirka musu harsasai. Kamar yadda rahotanni suka bayyana, wadanda ‘yan bindigan suka kaiwa hari ‘yan asalin kauyukan Bakin Kogi ne da Narido kuma suna hanyarsu ta zuwa kasuwar Bakin Kogi ne.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna damuwarsa a kan wannan harin tare da aikewa iyalan mamatan ta’aziyya. Gwamnan ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da sun yi bincike mai zurfi a kan aukuwar lamarin.