Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Harbe Uku Cikin ?aliban Jami’ar Da Suka Sace


Ma’aikatar tsaro ta jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce yan bindiga sun kashe dalibai uku na na Jami’ar Greenfield da aka sace a Jihar.

Cikin wani sakon Twitter da Ma’aikatar ta fitar ta ruwaito Gwamnan Jihar Nasir El-Rufa’i ya yi Allah-wadai da wannan mummunan rashin imani ga rayuwar dan adam.

Ya kara da cewa dole a yaki wadannan ‘yan bindiga ta ko wanne hali.

Ya kuma ce sharri ba zai taba yin nasara ba kan alheri. Ya kuma aika ta’aziyyarsa ga mutanen jihar da iyayen yaran da suka rasa yarukansu.

Kuma gwamnati za ta gaba da shaida wa mutanen jihar halin da ake ciki game da lamarin.

Related posts

Leave a Comment