Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa akalla mutane 15 ne suka rasa ransu a kauyen Kaya dake yankin Fitika na karamar hukumar Giwa dake jihar.
Lamarin ya farune bayan da ‘yan Bindiga suka shiga kauyen da Misalin daren jiya, Asabar inda kuma suka kone shaguna 11.
Da Misalin Karfe 8 na darene aka kai harin. Kuma mazauna garin sun bayyana cewa suna tsammanin harin ramuwar gayyane wanda matasan garin suka kaiwa wani shugaban ‘yan Bindigar da kuma kashe danginsa 2.
Kakakin ‘Yansandan jihar, Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar lamatin inda yace amma suna Allah wadai da daukar doka a hannu da wasu mutane ke yi akan wanda suke zargin masu garkuwa da mutanene.