Wani matafiyi mai suna Datti, ya ce shi da kan sa ya taimakawa ?an banga wajen kwashe wasu da harin ya ritsa da su, inda a gaban idonsa ya ga Gawarwakin 6.
Da take tabbatar da lamarin a wata sanarwa da shugabanta Barrister Salisu Haruna ya sa hannu, ?ungiyar ci gaban Birnin Gwari BEPU, ta ce ko a ranar Litinin ma, ?an bindigar sun tare hanyar a yankin na Zankoro da misalin ?arfe 9am na safe inda suka ri?a harbe-harbe sannan suka kwashe wasu mutane da ba a tantance yawansu ba.
Da aka tuntu?i kakakin rundunar ?an sandan jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ba su ce komai ba kan batun.
Lamarin tsaro dai a jihar Kaduna na ?ara shiga cikin wani mawuyacin hali a kusan kullum, inda satar mutane da yin garkuwa da su ke neman zama ruwan dare a kowace a rana, duk da han?oron da gwamnatin Jihar ke yi na cewar tana shawo kan matsalar.